Isa ga babban shafi

Jagororin mulkin Sojin Burkina Faso da Mali sun gana da juna kan sha'anin tsaro

Sabon shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya isa kasar Mali a ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun da ya dare karagar mulki, inda suka yi wata ganawa a kan sha'anin tsaro da zaman lafiya, wadda takwaransa Assimi Goita ya ce za ta haifi da mai ido.

Ganawar shugabannin mulkin Sojin kasashen Mali da Burkina Faso.
Ganawar shugabannin mulkin Sojin kasashen Mali da Burkina Faso. © Gouvernement malien
Talla

Kyaftin Traore, wanda ya karbe mulki a juyin mulkin ranar 30 ga watan Satumba, ya sauka kasar Mali ne a jiya Laraba don abin da ma’aikatar tsaron Mali ta kira tattaunawar abota ta sa’o’i 3.

Gabanin ziyarar ta Traore dai, jagoran Sojin na Burkina Faso ya ce bashi da shirin bin sahun Mali wajen daukar Sojin hayar kamfanin Wagner don taimakawa kasar a yaki da matsalar tsaro. 

Dukannin shugabannin sun kwace iko a kasashen su ne sakamakon yadda ayyukan ta’adanci suka ci gaba da addabar kasashen nasu, sai dai duk da matakin juyin mulkin har yanzu bata zani ba dangane da matsalar tsaron.

Ko a baya-bayan nan sai da dukkanin kasashen biyu suka fuskanci hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, lamarin da ya zama batu mafi girma da shugabannin biyu suka tattauna a kai yayin ganawar ta su a jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.