Isa ga babban shafi

Faransa ta amince ta janye sojinta daga Burkina Faso

Faransa ta sanar da shirin janye dakarunta daga Burkina Faso bayan bukatar hakan daga gwamnatin sojin Ouagadougou, lamarin da Ma'aikatar Wajen Paris ke cewa ilahirin dakarun kasar za su fice daga kasar cikin wata guda mai zuwa.

Dakarun Sojin Faransa da ke aikin yaki da ta'addanci a yankin Sahel.
Dakarun Sojin Faransa da ke aikin yaki da ta'addanci a yankin Sahel. © RFI/Mounia Daoudi
Talla

Wata sanarwar Ma'aikatar Wajen Faransar dauke da sa-hannun kakakinta ta ce, Burkina Faso ta mika bukatar janye dakarun a hukumance wanda ke kawo karshen yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla a shekarar 2018 da ta bayar da damar girke dakarun a kasar ta yankin Sahel.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, tuni Faransa ta aminta da bukatar ta Burkina Faso kuma za ta mutunta sharuɗɗan da ke kunshe a yarjejeniyar wadda ta kayyade wa'adin wata guda na ficewar dakarun bayan bukatar hakan daga bangare guda. 

Yanzu haka akwai dakarun Faransa 400 da ke sansanin soji na musamman can a yankin Sabre na Burkina Faso wadanda ke matsayin wani bangare na rundunar sojojin Faransar da ke aikin yaki da ta'addancin mayaka masu ikirarin jihadi a yankin Sahel. 

Kafin wannan mataki dai, gwamnatin Burkina Faso karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore ta bai wa uwar goyonta tabbacin cewa ba za tabi sahun Mali wajen dauko sojojin hayar Wagner zuwa kasar ba, sai dai wasu bayanai sun bayyana cewa tuni wakilcin Kamfanin Tsaron mallakin Rasha ya kai ziyara kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.