Isa ga babban shafi

Mu muka kori dakarun Faransa daga kasarmu - Sojin Burkina Faso

Gwamnatin Burkina Faso ta ce, lallai ita ce ta bukaci Faransa da ta janye dakarunta daga kasar mai fama da ta’addanci  nan da wata guda.

Ibrahim Traoré, jagoran gwamnatin sojin Burkina Faso tare da jami'an tsaronsa.
Ibrahim Traoré, jagoran gwamnatin sojin Burkina Faso tare da jami'an tsaronsa. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso Jean-Emmanuel Ouedraogo ne ya bayyana haka a yayin wata hira da gidan rediyo da talabijin mallakin kasar a yau Litinin.

Wannan umarni da kasar ta bayarwa shi ne sabon al’amari da ke kara tabbatar da tabarbarewar alaka tsakanin Burkina Faso da uwar goyonta Faransa, tun bayan juyin mulkin watan Satumban bara. 

A cewar ma’aikatar watsa labaran Burkina Faso, gwamnatin sojin ta yi watsi da wata yarjejeniyar jibge sojojin Faransa a kasar da aka kula tsakanin kasashen biyu a 2018, inda kuma ta ba su wa’adin wata guda su bar kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.