Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta bukaci dakarun Faransa su fice daga kasar

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta umarci sojojin Faransa da ke jibge a kasar da su tattara nasu ya nasu su bar kasar cikin wata guda. 

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso,  Ibrahima Traoré.
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahima Traoré. © Kilaye Bationo / AP
Talla

Wannan umarni da kasar ta bayar shine sabon al’amari da ke kara tabbatar da tabarbarewar alaka a tsakanin Burkina Faso da uwar goyonta Faransa, tun bayan juyin mulkin watan Satumban bara. 

A cewar ma’aikatar watsa labaran Burkina Faso, gwamnatin sojin ta yi watsi da wata yarjejeniyar jibge sojojin Faransa a kasar da aka kula tsakanin kasashen biyu a 2018, inda kuma ta basu wa’adin wata guda su bar kasar. 

Kamfanin dillancin Labaran Faransa  ya ruwaito cewa ya zuwa yanzu dai babu wani martini game da wannan sabon Lamari daga Paris. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.