Isa ga babban shafi

Masu ikirarin jihadi sun yi awon gaba da mata 50 a Burkina Faso

Wasu da ake zargi mayaka masu ikiraarin jihadi ne sun yi awon gaba da wasu mata 50 a arewacin Burkina Faso da ake yawan samun rikice rikice.

Taswirar kasar Burkina Faso da ke fama da matsalar ta'addamci.
Taswirar kasar Burkina Faso da ke fama da matsalar ta'addamci. © RFI
Talla

Wasu jami’an yankin da suka tabbatar da aukuwar lamarin sun ce maharan sun sace kimanin mata 40 a kudu maso gabashin garin Arbinda a ranar Alhamis, kana suka dauke 20 a arewacin garin.

Majiyoyin daga yanki sun ce akwai mata da dama da suka tsere wa maharan.

Sun karaa da cewa matan sun tafi daji ne don neman ‘yayan itace da ganyayyaki da za su ci, duba da matsalar yunwa da ta addabe su a yankin.

Wani jami’in yankin da ya tabbatar da sace matan ya ce sojoji da masu aikin as kai sun yi kokarin  ceto matan amm abin ya faskara.

Garin Arbinda  yana yankin Sahel ne a arewacin Burkina Faso, yankin da mayaka masu ikirarin jihadi suka wa kawanya, lamarin da ya sa ake fama da karancin  abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.