Isa ga babban shafi

‘Yan ta’adda sun kashe mutane tara a wani masallaci a Burkina Faso

An kashe mutane tara a yammacin jiya laraba a wani hari da wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wani masallaci a arewa maso gabashin Burkina Faso, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito a yau Alhamis.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

A cewar wani shaida, masu yan ta’addan sun isa kauyen Goulgountou, kusa da Falagountou a kasar ta Burkina Faso, suna kan babura takwas, kafin su afka musu a cikin masallacin.

‘Yan ta’addan sun raba mata da yara da tsoffi kafin su yi wa'azi tare da bukatar ganin mutanen garin sun yi watsi da imaninsu, har ma an fara tattaunawa da liman kuma hakan ya biyo bayan kin amincewarsa ne aka kashe na kashewa.

Sun yi kokarin kashe liman, amma ya bijire cewa yana son ya mutu a tsaye, sai 'yan ta'addan suka harbe shi a kai," in ji wani mazaunin yankin da ya halarci jana'izar wadanda aka kashe.

Ya kara da cewa "An harbe wasu masu ibada takwas, musamman shugabannin al'umma.

Mahukuntan da ke yankin Falagountou, wanda ke da babban wurin hakar zinare na Essakane, na fuskantar kutse da dama daga wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne tun farkon wannan makon.

A cewar majiyoyin yankin, mazauna kauyen da dama sun tsere daga kauyen tun bayan afkuwar lamarin zuwa wasu yankunan da ake ganin sun fi tsaro.

Kasar Burkina Faso, musamman a yankin arewacin kasar, tun daga shekarar 2015, ta fuskanci karuwar hare-hare daga kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kuma kungiyar IS.

Lamuran da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba akalla miliyan biyu da muhallansu.

Kyaftin Ibrahim Traoré, shugaban rikon kwarya da ya hau kan karagar mulki biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 30 ga watan Satumba  ya dau niyar kwato yankunan kasar  da gungun 'yan ta'adda suka mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.