Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta musanta zargin biyan sojin Wagner na Rasha da lasisin hakar zinare

Ministan ma'adinai na Burkina Faso ya musanta zargin da shugaban Ghana ya yi na cewa kasar na biya sojojin haya Wagner na Rasha da mallaka musu wuraren hakar  ma'adinai.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Kyaftin  Ibrahim Traoré.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré. AFP - -
Talla

Ministan ma'adinai Simon Pierre Boussim ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, "Ba su ba da izinin hakar ma’adanai ga wani kamfani na Rasha a kudancin Burkina ba."

Ikirarin da Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo yayi a makon da ya gabata cewa Burkina Faso ta dauki sojojin haya daga kamfani Wagner na Rasha don taimaka mata wajen yaki da masu dauke da makamai ya haifar da cece-kuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.