Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso sun kori babbar jami'ar MDD

Gwamnantin mulkin sojin Burkina Faso ta bukaci shugabar ofishin Majalisar Dinkin Duniya ‘yar asalin Italiya da ta gaggauta ficewa daga kasar da ke cikin yanayi na bukatar agaji saboda matsalolin masu nasaba da ayyukan ta’addanci.

Shugaban sojin da ke mulki a Burkina Faso, Ibrahima Traoré
Shugaban sojin da ke mulki a Burkina Faso, Ibrahima Traoré © Kilaye Bationo / AP
Talla

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Burkina ta Faso ta fitar a wannan Juma’a, ta bukaci Barbara Manzi da ta tattara nata-ya-nata domin ficewa daga kasar, saboda yadda ta sallami wasu da ke yi wa majalisar aiki ba tare da ta nemi jin ta bakin mahukuntan kasar ba.

Sanarwar ta ce,, daukar matakin gaban-kai da Barbara ta yi, ba wani abu ba ne face reni da kuma kokarin tozartar da kimar Burkina a idon duniya, tare da karya gwiwar wadanda ke sha’awar zuba jari a kasar.

‘’Matakin da Uwargida Manzi ta dauka, ba abin da zai haifar wa Burkina Faso face jefa ta a cikin mawuyacin hali a watanni masu zuwa, kuma kawo yanzu ba mu fahinci dalilinta na daukar matakin ba’’ a cewar sanarwar.

Ko shakka babu dai Burkina Faso na bukatar tallafin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji domin tunkarar kalubale na tsaro saboda ayyukan ta’addanci.

Kawo yanzu dai babu wani martaki daga Majalisar ta Dinkin Duniya ta fitar dangane da matakin korar babbar jami’ar daga birnin Ouagadougou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.