Isa ga babban shafi

An gano gawarwaki 28 a arewa maso yammacin Burkina Faso

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce an gano gawarwaki 28 a arewa maso yammacin kasar, inda kuma ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wanda ke da alhakin halaka mutanen.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

An dai gano gawarwakin mutanen 28 ne a daren ranar 30 zuwa 31 ga Disamba.

Hare-haren da ake kaiwa jami'an tsaro da fararen hula na karuwa a 'yan watannin nan, musamman a yankunan arewaci da gabashin kasar da ke kan iyaka da Mali da Nijar, kasashen da su ma suke fafatawa da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Daya daga cikin kungiyoyin fararen hular da ke rajin kare hakkin dan Adam a Burkina Faso, mai CISC, ta yi tir da kisan, tare da tuhumar sojojin sa-kai na VDP da gwamnati ta kafa da aikata kisan, a matsayin ramuwar gayya kan farar hula da ba sa ga maciji.

Burkina Faso dai ta riga ta fuskanci juyin mulki guda biyu da sojoji suka yi a shekarar bana.

Tun a shekara ta 2015 kasar ke fama da da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da suke alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS wadanda suka kashe dubun-dubatar mutane, tare da raba wasu kusan miliyan biyu da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.