Isa ga babban shafi

Fiye da matasa dubu 90 sun mika bukatar zama Sojojin sa kai a Burkina Faso

Gwamnatin Sojin da ke mulki a Burkina Faso ta ce yanzu haka akwai matasa fiye da dubu 90 daga sassan kasar wadanda suka amsa kiran shiga aikin sa kai don taimakawa Sojojin da ke yaki da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Wasu Matasa a Burkina Faso.
Wasu Matasa a Burkina Faso. AP - Sophie Garcia
Talla

Cikin watan Oktoban da ya gabata ne Burkina Faso ta sanar da shirin daukar sojojin sa kai dubu 50 don taimakawa dakarun Sojin kasar a kokarin yakar ‘yan ta’addan da suka hana zaman lafiya,

Gwamnatin Sojin ta Burkina Faso karkashin jagorancin Kaftin Ibrahim Traore da ya jagoranci juyin mulkin kasar na baya-bayan nan, ta ce matasa dubu 35 daga cikin mayakan sa kan dubu 50 da za ta dauka za su bayar da tsaro ne a yankunansu yayinda wasu dubu 15 kuma za a rarrabasu a wasu sassa na kasar.

Sai dai sanarwar da Ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce maimakon mayaka dubu 50 da suka bukata yanzu haka matasa fiye da dubu 90 ne suka mika bukatar shiga aikin na sakai.

Kwamandan da ke kula da rundunar ‘yan kishin kasa a Burkina Faso Laftanal Kanal Thomas Sawadogo, ya yabawa matasan kasar wadanda ya ce a shirye su ke su bayar da gudunmawa don kawar da matsalar tsaron da ta addabi kasar.

A ranar 18 ga watan Nuwamban da muke ciki ne aka kammala tattara sunayen wadanda za su shiga aikin sa kan inda laftanal kanal Sawadogo ke cewa za su karbi horon kwanaki 14 daga rundunar Sojin kasar gabanin rarraba su zuwa yankunan da za su yi aiki.

Burkina Faso wadda ke fama da hare-haren ta’addanci tun shekarar 2015 daga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi ciki har da Al-Qaeda da IS tun bayan faro hare-harensu a arewacin kasar da gabashi sun tialstawa iyalai fiye da miliyan biyu barin matsunansu yayinda suka kashe dubunnai ciki har da tarin fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.