Isa ga babban shafi

Burkina faso na duba yiwuwar karfafa alakarta da kasar Rasha

Burkina Faso ta ce akwai yiwuwar sake yin narari a game da alakar da ke tsakanin kasar da kuma Rasha, musamman lura da irin hali na rashin tsaro da kasar ke fama da shi sakamakon bayyanar kungiyoyin ta’addanci.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Firaministan Burkina Faso Appolinaire Kyelem de Tembela, shi ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta kasar cikin daren lahadi, a matsayin martani ga mutanen da ke gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan ga keftin Ibrahim Traore wanda ya karbi ragamar mulkin kasar a karshen watan satumbar da ya gabata.

Firaminista de Tembela, ya ce tun a shekarar 1967 ne aka yi wa yarjejeniyar da ke tsakanin Burkina Faso da tsohuwar Taryyyar Sobiet bitar karshe, saboda haka ba wai sai jama’a sun gudnar da zanga-zangar neman samun kusanci a tsakaninsu ba, domin kuwa dama akwai wannan alaka tsakanin kasashen biyu.

Ya ci da cewa ‘’watakila saboda yanayin da kasar ke ciki a yau, akwai yiwuwar a sake zaunawa domin kulla sabuwar yarjejeniya domin kare muradun kasar ta Burkina Faso, to sai ya kara da cewa ‘’hakan ba wai yana nufin cewa suna karbar umurni daga masu zanga-zanga a kan tinti ba ne’’.

Appolinaire Kyelem de Tembela, ya ce idan dai har masu zanga-zangar suna yi ne saboda kishin kasa, to ya kamata su nuna kiyayya ga ‘yan ta’adda ne, tare da nuna wa jami’an tsaron kasar goyon baya ciki har da samar da kudade da kuma kayan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.