Isa ga babban shafi

Ana farautar mayakan da suka sace mata 50 a Burkina Faso

Jami’an tsaro sun fara farautar mayakan jihadin da suka sace  mata 50 a yankin arewacin Burkina Faso mai fama da tashe-tashen hankula kamar yadda gwamnan jihar ya bayyana a yau Litinin.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

Jami’an tsaron kasar sun ce, suna amfani da hanyoyin sama da na kasa da zummar gano matan.

An sace matan ne a mabanbantan hare-haren da mayakan suka kaddamar a ranar Alhamis da Juma’a da suka gabata a daidai lokacin da suka fito neman abinci.

Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gaggauta sakin wadannan mata ba tare da gindaya wasu sharudda ba, tana mai bukatar hukumomi da su nemo ‘yan ta’adda tare da hukunta  su.

Burkina Faso wadda kasa ce da ke kewaye da kan iyakoki na kasa, na fama da  matsalar ta’adanci tun shekara ta 2015, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane,  baya ga miliyan biyu da suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.