Isa ga babban shafi

France 24 ta yi tir da dakatar da ita a Burkina Faso

Daga  birnin Paris, hukumar gudanarwa  tashar France 24, wato France Medias Monde ta mayar da martini kan dakatar da ita da gwamnatin Burkina Faso ta yi, tana mai bayyana matakin a matsayin wuce gona da iri da bata suna, tana mai cewa, zargin da ake mata ba shi da tushi ballantana makama.

Ginin France Medias Monde, mai kula da tashar France 24,
Ginin France Medias Monde, mai kula da tashar France 24, Anthony Ravera
Talla

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta dakatar da tashar talabijin ta France 24 daga watsa shirye shiye a kasar, biyo bayan wata ganawa da ta yi da shugaban kungiyar Al-Qaeda, shiyyar arewacin Afrika.

Burkina Faso, wadda ke fama da matsalar ta’addanci da ta samo asali daga makwafciyarta Mali, ta ce bai wa ‘yan ta’adda dama da tashar Francce 24 ta yi tamkar amimcewa da ta’asar da take yi ne.

Kakakin gwamnatin Sojin kasar, Jean Manuel Ouedraogo  ya bayyana haka ne, yana mai nuni da ganawar da tashar talabijin ta France 24 ta yi   da shugaban Al-Qaeda ta arewacin Afrika, Abu Ubaydah Yusuf al-Annabi a ranar 6 ga watan Maris.

France 24 ta  jaddada cewa ba kai tsaye aka watsa ganawar  shugaban Al-Qaeda a tashar ba, illa amfani da ganawar  ta yi wajen tabbatar da cewa kungiyarsa ce ta yi garkuwa da dan jaridar nan  bafaranshe da aka sako a makon da ya gabata a Jamhuriyar Nijar.

Tarayyar Turai, ta bakin jagoran diflomasiyyarta, Josep Borrell ta caccaki matakin gwamnatin sojin Burkina Faso,  tana mai cewa babu adalci a  cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.