Isa ga babban shafi

Sojin Burkina Faso sun kawo karshen zaman dakarun Faransa a kasar

Gwamnatin sojan Burkina Faso ta kawo karshen zama tare da ayyukan sojojin Faransa a kasar, matakin da ta sanar da aiwatar da shi a hukumance ranar Lahadin da ta gabata, bayan bikin sauke tutar dakarun na Faransa da aka yi a babban sansaninsu dake kasar.

Shugaban kasar Burkina Faso Laftanar Kanal Paul-Henri Damiba.
Shugaban kasar Burkina Faso Laftanar Kanal Paul-Henri Damiba. via REUTERS - BURKINA FASO PRESIDENCY
Talla

A watan Janairu sojojin Burkina Faso suka bai wa Faransa wa'adin wata guda da ta janye sojojinta, tare da kawo karshen yarjejeniyar aikin sojin da ta bai wa dakarun Faransar damar yakar 'yan ta’adda a cikin kasar.

Ficewar sojojin Faransa daga Burkina Faso dai ya budewa kasar sabon babi ne a yakin da take yi da kungiyoyin ‘yan ta’addda masu alaka da al Qaeda da IS, wadanda suka mamaye yankuna da dama tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Tabarbarewar dangantaka tsakanin Faransa da sojojin Burkina da suka karbe ragamar jagorancin kasar bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaba, Roch Marc Christen Kabore, shi ne dalilin da ya assasa ficewar sojin Faransawan na musamman guda 400 daga kasar ta Burkina.

A shekarar da ta gabata, zanga-zangar da masu adawa da sojojin Faransa ke yi ta yi karfi, ganin cewa sun gaza murkushe ‘yan ta’adda da suka addabi al’ummmar Burkina musamman a yankin arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.