Isa ga babban shafi

Faransa ta kira jakadanta na Burkina Faso kan dambarwar kasashen biyu

Faransa ta sanar da kiran jakadanta daga Burkina Faso kwana guda bayan amincewa da janye ilahirin dakarunta da ke aikin yaki da ta’addanci a kasar ta yankin Sahel.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - BENOIT TESSIER
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce za ta kira jakadan na ta ne don tuntuba game da makomar alakar kasashen biyu, wadda ke nuna yiwuwar samun farraka kwatan-kwacin wadda Faransar ta samu tsakaninta da Mali.

Faransa wadda ke matsayin uwar goyon Burkina Faso a shekarar 2018 ne suka kulla yarjejeniyar da ta kai ga girke dakarun Sojin don yaki da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar ta yankin saharar Afrika.

Kafin yanzu dai Burkina Faso ta baiwa Paris tabbacin cewa alaka bazata munana tsakaninsu ba, sai dai a baya-bayan nan wasu bayanai sun bayyyana yadda kasar ke kokarin karkatawa waje kulla alaka da Rasha, lamarin da ka iya rushe alakarta da uwar goyon na ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.