Isa ga babban shafi

Faransa ta kwashe 'yan kasarta Iyalan mayakan ISIL daga Syria

Faransa ta sake kwashe mata 15 da yara 32 daga wani sansani da aka killace mutanen da ake zargin mayakan jihadi ne can a Syria, wanda ke matsayin karo na 3 da Paris ke kwaso al’ummarta wadanda suka je yaki gabas ta tsakiya. 

Wasu mata a sansanin 'yan gudun hijira na Syria.
Wasu mata a sansanin 'yan gudun hijira na Syria. AFP
Talla

Aikin kwashe matan da kananan yaran ya zo ne bayan matsin lambar da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke yiwa Faransar tsawon shekaru game da yadda al‘ummarta wadanda ke matsayin iyalai ga mayakan IS da ko dai aka kashe su ko kuma aka kame su ke ci gaba da zama a sansanin da aka killace wadanda ake yiwa zargin zama da mayakan jihadin. 

A lokuta da dama dai gwamnatin Faransa na watsi da kiraye-kirayen kwaso mutanen wadanda ta ce shigarsu Paris barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar al’ummarta la’akari da hare-haren ta’addancin da kasar ta gani a 2015. 

Sai a yau talata, ma’aikatar wajen kasar ta sanar da aikin kwaso mata akalla 15 da yaransu 32 wadanda suka shiga yaki Syria gabanin wargaza sansaninsu da ke ikirarin kafa daular musulunci a shekarar 2019. 

Aikin kwaso mujahidan Faransawar 15 da yaransu 32 kari ne kan makamancinsa da ya gudana a watan Yulin 2022 da ya kai ga kwaso mutane 55. 

Kafin aikin kwashe iyalan mujahidan a yau talata akwai Faransawan akalla 150 da suka kunshi ke sansanin.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.