Isa ga babban shafi

Ya kamata Putin ya kawar da Kurdawan da ke iyakar Syria - Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shaidawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa ya zama wajibi fadar Kremlin ta kawar da mayakan Kurdawa daga Arewacin Syria.

Shugaban turkiyya Reccip Tayyip Erdogan da takwaransa na Rasha vladmir Putin kenan
Shugaban turkiyya Reccip Tayyip Erdogan da takwaransa na Rasha vladmir Putin kenan via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Erdogan dai ya sha yin barazanar kaddamar da wani sabon kutse a arewacin Syria domin fatattakar dakarun Kurdawan da ya dora wa alhakin harin da aka kai a watan Nuwamban wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida a Istanbul.

Yarjejeniyar 2019 tsakanin Moscow da Ankara ta kawo karshen wani harin ta hanyar kafa wani yanki mai tsaro mai tsawon kilomita 30 don kare Turkiyya daga hare-haren wuce gona da iri daga mayakan Kurdawa.

Erdogan ya zargi Rasha da taka muhimmiyar rawa a rikicin Syria da ke goyon bayan shugaba Bashar al-Assad wanda ta ce ya gaza wajen mutunta yarjejeniyar.

Shugaban na Turkiyya ya shaida wa Putin a wayar tarho cewa yana da muhimmanci a share mayakan Kurdawa daga kan iyaka zuwa nisan akalla kilomita 30.

Rahotanni na cewa, wasu daga cikin dakarun Kurdawa suna jibge a yankunan da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar tabbatar da tsaro a Arewacin Syria ta wayar tarho.

Moscow da Washington sun yi ta matsin lamba na diflomasiyya kan Ankara kan kada ta kaddamar da wani sabon yaki ga mayakan Kurdawan.

Tun a ranar 20 ga watan Nuwamba ne Turkiyya ta yi ta luguden wuta kan wuraren Kurdawa da ke kusa da kan iyakar Syria da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.