Isa ga babban shafi

A karon farko kasashen Turkiyya da Syria sun yi taro a Rasha

Ministocin tsaron kasashen Rasha, Turkiyya da Syria sun gana a birnin Moscow, wanda shi ne tattaunawa ta farko tun bayan barkewar yakin Syria, in ji ma'aikatar tsaron Rasha.

Recep Tayyip Erdogan tare da Vladimir Putin
Recep Tayyip Erdogan tare da Vladimir Putin AP - Vyacheslav Prokofyev
Talla

Wannan dai ita ce ganawar farko da ministocin tsaron Turkiyya da na Syria suka yi tun bayan fara yakin a shekara ta 2011.

Rasha da Turkiyya na goyon bayan Syria, inda Moscow ke goyon bayan gwamnatin Damascus a kan 'yan adawar ta, sannan Ankara na goyon bayan 'yan tawaye.

Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha yin barazanar kaddamar da farmakin soji a arewacin Syria kan kungiyoyin Kurdawa.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu da takwarorinsa na Turkiyya da Syria Hulusi Akar da Ali Mahmoud Abbas sun tattauna kan hanyoyin warware rikicin Syria, da matsalar 'yan gudun hijira, da kokarin hadin gwiwa na yakar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Syria.

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta yi irin wannan bayanin, inda ta ce an gudanar da taron cikin yanayi mai kyau, domin kawo karshen matsalar tsaron da mayakan Kurdawa ke haifarwa.

Ministocin harkokin wajen Turkiyya da Syria sun yi wata ‘yar gajeriwar musayar ra’ayi a gefen taron yankin a shekarar 2021 kuma Ankara ta amince da tuntubar juna tsakanin hukumomin leken asirin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.