Isa ga babban shafi

Dakarun Burkina Faso sun kashe sama da 'yan ta'adda 100 a arewacin kasar

Rundunar sojin Burkina Faso ta ce dakarunta sun  kashe ‘yan ta’adda 112 a jerin gwabzawa da suka yi a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ita ma ta yi asarar mayakanta 11.

Dakarun Burkina Fasoa  arewacin kasar da ke fama da matsalar ta'addanci.
Dakarun Burkina Fasoa arewacin kasar da ke fama da matsalar ta'addanci. © OLYMPIA DE MAISMONT / AFP
Talla

Wata sanarwa daga rundunar sojin ta ce an kadamar da jerin samame a lokaci guda  da zummar sake kwato yankunan da ke hannun ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin kasar ba tare da bayyana takamammen lokacin wadannan samame ba.

Baya ga kashe wadannan ‘yan ta’adda, sojin Burkina Faso ta kuma  lalata tare da karbe dimbim makamai, motoci da Babura da kuma ababe masu fashewa.

Sanarwa sojin ta kara da cewa dakarun gwamnatin sun samu nasarar kwato yankuna da dama sakamakon wadannan hare hare da aka shafe kwanaki ana kai wa ‘yan ta’adda.

A cikin farkon wannan watan na Maris, mayaka masu ikirarin jihadi sun kashe fararen hula da dama, sai dai duk da cewa gwamnati ba ta bayyana adadin wadanda aka kashe ba, wata kungiyar kare hakkin dan adam ta ce sun kai 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.