Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kulle mahakun ma'adinai 43 saboda hare-haren ta'addanci

Burkina Faso ta sanar da dakatar da aikin wasu mahakun ma’adinai fiye da 40 saboda barazanar tsaron da ke ci gaba da tsananta a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wasu mahaku a Burkina Faso.
Wasu mahaku a Burkina Faso. REUTERS - Katrina Manson
Talla

Burkina Faso na sahun kasashen yammacin Afrika da ke fama da hare-haren ta’addanci tun shekarar 2015 wanda zuwa yanzu ya kashe mutane fiye da dubu 10 baya ga tilastawa wasu fiye da miliyan 2 tserewa daga matsugunansu.

Mahukuntan yankin Boucle du Mouhoun da ke arewa maso yammacin Burkina Faso sun sanar da kulle mahakun ma’adinai 43 a wani yunkuri na dakile tasirin ‘yan ta’adda da kuma kare rayukan ma’aikatan da ke aikin a wuraren.

Gwamnan yankin Babo Pierre Bassinga ya ce mahakun za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da za a bayar da umarnin daidaituwar al’amura a yankin.

A kalamansi yayin sanarwar kulle mahakun, Gwamna Babo Pierre Bassinga ya ce duk wanda aka samu da laifin ci gaba da aiki a mahakun kai tsaye za a tuhume shi da taimakawa ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.