Isa ga babban shafi

Burkina Faso za ta dauki sabbin Sojoji dubu 5 don yakar ta'addanci

Burkina Faso ta sanar da shirin daukar sabbin sojoji na musamman guda dubu 5 don taimakawa dakarun da ke yaki da ayyukan ta’addanci a kasar mai fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi tun shekarar 2015.

Dakarun Sojin Burkina Faso.
Dakarun Sojin Burkina Faso. AFP/File
Talla

Sanarwar da ma’aikatar Sojin ta fitar ta ce dakarun dubu 5 za su yi aikin akalla shekaru 5-5, don fatattakar barazanar ta’addanci a yankunan kasar 15, dai dai lokacin da ake ci gaba da asarar sojoji a fagen daga.

Karkashin dokokin aikin Sojan da Burkina ta gindaya wajibi ne masu neman aikin su zama an haife su tsakanin shekarar 1988 zuwa 2003.

Ko a watan Aprilu sai da Burkina Faso ta dauki sojoji dubu 3 aiki don taimakawa wajen yakar ta’addancin said ai a baya-bayan nan kasar na ci gaba da asarar dakaru a hannun ‘yan ta’adda.

Ko a jiya sai da ‘yan ta’adda suka kashewa Burkina Faso sojojin sa kai 15 kari kan wasu kusan 70 da aka kashe a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.