Isa ga babban shafi

Wani kamfanin Isra'ila ya yi yunkurin bata sunan ICRC a Burkina Faso - Rahoto

Wani bincike ya nuna cewa wani kamfani mallakar kasar Isra'ila ya yi yunkurin bata sunan kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) a Burkina Faso, mai yiwuwa bisa bukatar gwamnatin Burkina Faso a shekarar 2020.

Mutanen 71 da aka janye daga Yemen suna wakiltar fiye da rabin ma'aikatan ICRC na kasa da kasa a kasar
Mutanen 71 da aka janye daga Yemen suna wakiltar fiye da rabin ma'aikatan ICRC na kasa da kasa a kasar AFP
Talla

Rahoton da wata gamayyar kungiyoyin 'yan jarida karkashin jagorancin wata kungiya mai zaman kanta ta Faransa, ya bayyana cewa kamfanoni masu zaman kansu a duniya suna amfani da kutse da shafukan sada zumunta wajen yin amfani da ra'ayin jama'a domin bata sunan wasu kungiyoyin.

Gamayyar kungiyoyin da ke kasancewa a matsayin abokan hulda sun gana da daya daga cikin shugabannin biyu na kamfanin Percepto International na Isra'ila, Royi Burstien, wanda ya ambaci Burkina Faso a matsayin nasarar yakin neman zaben da kamfaninsa ya yi.

Burkina Faso dai na cikin rikicin da ya dauki tsawon shekaru bakwai ana gwabzawa da 'yan ta’adda, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba akalla mutane miliyan biyu da muhallansu.

A cikin yakin neman zaben da ake zargin, wani yanki na ra'ayi ya bayyana a cikin mujallar Faransa ta Valeurs Actuelles a ranar 3 ga Agusta, 2020, yana neman bahasi kan ko ICRC ke daukar nauyin ta’addanci a Burkina Faso."

Kafofin yada labaran Burkina Faso ne suka yada labarin kuma hakan ya haifar da mummunar takaddamar adawa da ICRC da kafafen sada zumunta suka yi, wanda ya haifar da fargabar kare lafiyar ma’aikatan ICRC da ke aiki a kasar.

ICRC a shafinta na Internet ta ayyana kanta a matsayin kungiyar mai zaman kanta, da ke tabbatar da kariya ga bil adama da taimako ga wadanda rikici ya rutsa da su.

Rahoton na baya-bayan nan na kungiyar ya biyo bayan wani labari da ke cewa wani kamfani na Isra'ila, mai suna "Team Jorge", ya yi tasiri ga fiye da zabuka 30 a duniya don abokan ciniki ta hanyar yin kutse, zagon kasa da yada labaran karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.