Isa ga babban shafi

MSF ta dawo da ayyukanta a sassan Burkina Faso bayan kisan jami'anta

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF ta sanar da shirin dawo da ayyukanta na jinkai a sassan Burkina Faso, makwanni 3 bayan dakatarwa sakamakon kisan jami’anta 2 da ‘yan ta’adda suka yi a arewacin kasar.

Wasu jami'an kungiyar agaji ta MSF.
Wasu jami'an kungiyar agaji ta MSF. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Kungiyar agajin ta Faransa MSF ko kuma Doctors Without Borders da ke aiwatar da ayyukan agaji a kasashen da ke fama da rikici, a ranar 17 ga watan Fabarairu ne ta sanar da dakatar da ayyukanta a sassan Burkina Faso bayan harin ranar 8 ga watan da ya kasha jami’anta 2.

Wani sako da MSF ta wallafa a shafinta na Twitter jiya laraba, ta ce za ta ci gaba da ayyukanta a sassan Burkina Faso don taimakawa wadanda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa musamman a tsakiyar kasar.

MSF ta ce wajibi ne ta nuna sadaukarwa ga jami’anta da suka rasa rayukansu a harin ‘yan ta’addan amma hakan ba zai hana ta ci gaba da ayyukan kai dauki sassan Burkina Fason da ke fama da hare-haren ta’addancin ba.

Burkina Faso guda cikin kasashen matalauta a nahiyar Afrika tun a shekarar 2015 ta fara ganin hare-haren ‘yan ta’adda  wanda zuwa yanzu ya kasha mutane fiye da dubu 10 ciki har da Sojoji da ‘yan sanda baya ga fararen hula.

Wasu alkaluma sun nuna cewa fiye da kasha 40 na sassan kasar yanzu haka basa karkashin ikon gwamnatin kasar duk da juyin mulkin Soji har sau 2 da kasar ta gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.