Isa ga babban shafi

Harin 'yan ta'adda ya kashe mutane 15 a gabashin Burkina Faso

Majiyoyin tsaro a Burkina Faso sun ce ‘yan ta’adda sun kashe mutane 15 cikinsu kuma har da wasu jami’an tsaron sa-kai 3 yayin wasu hare-hare da suka kai jere da juna a yankin gabashin kasar.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan, yayin wani taro da ya hallara a birnin Ouagadougou, ranar 15 ga watan oktoba, 2022.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan, yayin wani taro da ya hallara a birnin Ouagadougou, ranar 15 ga watan oktoba, 2022. © Kilaye Bationo / AP
Talla

Wani mazaunin yankin ya shai da wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an kai hare-haren ne a karshen makon da ya gabata, a wasu kauyuka da suke karkashin Diapaga, babban birnin lardin Tapoa da ke gabashin Burkina Faso. 

Tun bayan fara fuskantar matsalar ta’addanci daga shekarar 2015, alkaluma sun nuna cewar zuwa yanzu mutane sama da dubu 17 akasarinsu fararen hula da kuma sojoji ‘yan ta’addan suka kashe a sassan Burkina Faso, cikinsu kuma har da fiye da dubu 6 da maharan suka kashe a shekarar bana kadai. 

Ya zuwa yanzu, sakam da fararen hula da sojoji 17,000 aka kashe a shekaru takwas da suka gabata, ciki kuwa har da adadin mutum 6,000 da aka kasha a shekarar 2023, kamar yadda wata kkungiya mai zaman kanta ta Acled ta tabbatar.

Rikicin masu dauke da makamai, ya tilastawa sama da mutum miliyan biyu tserewa daga muhallansu, a cewar alkaluman hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.