Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci gudanar da bincike kan kisan fararen hula sama da 100 a Burkina Faso

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan "kashe-kashen da aka yi a Burkina Faso cikin wannan watan, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ciki har da kananan yara.

Wani sojan Burkina Faso yayin horo. 14/03/2023
Wani sojan Burkina Faso yayin horo. 14/03/2023 © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Mai shigar da kara na gwamnatin Burkina Faso, a ranar litinin da ta gabata ya ce sama da mutane 70 ne aka kashe yayin wani hari da aka kai Zaongo da ke tsakiyar arewacin kasar a ranar 5 ga watan Nuwamba, kuma yawancinsu yara ne da kuma tsofaffi.

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana "bin diddigin munanan rahotannin kashe-kashen da aka samu a kasar da ke yammacin Afirka.

Kaddamar da bincike

"Muna kira ga gwamnatin rikon kwarya da su gudanar da cikakken bincike, mai zaman kansa, da kuma gaskiya kan wadannan rahotanni masu tada hankali," in ji mai magana da yawun Liz Throssell a cikin wata sanarwa.

Jami’ar ta ce mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 70, amma wasu rahotanni sun nuna cewa adadin wadanda aka kashe sun haura 100, inda wasu da dama jikkata".

Masu ikirarin jihadi a Mali

Kasar dai na fama da hare-haren daga masu ikirarin jihadi da ya samu asali daga makwabciyar kasar Mali a shekarar 2015 da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da sojoji sama da dubu 17 tare da raba mutane miliyan biyu da muhallansu.

Gwamnatin rikon kwaryan soji ke mulkin Burkina Faso tun bayan juyin mulkin da suka yi a watan Satumban 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.