Isa ga babban shafi

EU ta bukaci gudanar da bincike akan kisan gillar wasu fararen hula 100 a Burkina Faso

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a gudanar da bincike akan wani kinsan gilla da aka yi wa wasu fararen hula a Burkina Faso.

Jagoran diflomasiyyar Kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell
Jagoran diflomasiyyar Kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell AP
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar mai magana da yawun jami'in harkokin wajen kungiyar EU Josep Borrell ya bayyana cewa Kusan fararen hula 100 da suka hada da mata da kananan yara ne aka yi imanin an kashe a wannan kisan gillar da aka yi a kauyen Zaongo kwanaki da suka gabata a tsakiyar gabashin Burkina Faso.

Kungiyar tarayyar turan ta bukaci gwamnatin rikon Burkina faso da ta tabbatar ta gudanar da bincike domin samun hakikanin dalilin da ya haddasa kisan gillar.

Kasar da ke yammacin Afirka na fama da matsalar yaki da masu ikrarin jihadi da ya tamtsama cikin kasar daga makofciyar ta Mali tun a shekarar 2015 wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane sama da dubu 17 tare da raba dumbin wasu da matsugunan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.