Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane 70 a Burkina Faso

Mahukunta a Burkina Faso sun ce akalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai a wani kauye mai suna Zaongo da ke Yankin Arewa ta Tsakiya da ke kasar wadda ta jima tana fama da hare-haren masu ikirarin jihadi. 

Wani kauye da aka kai wa hari a Burkina Faso
Wani kauye da aka kai wa hari a Burkina Faso © via REUTERS - PRIME MINISTER'S PRESS SERVICE
Talla

 

A sanarwar da ya fitar a marecen Litinin, mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Burkina Faso Simon Gnanou. ya ce ‘yan bindigar sun kai wannan hari ne a ranar 5 ga wannan wata inda suka kashe kauyawa 70 sannan suna cinna wa gidaje da kadaro wuta. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa sai a ranar 11 ga wannan wata na Nuwamba ne masu bincike suka samu nasarar isa inda lamarin ya wakana, kuma kididdiga ta tabbatar da mutuwar mutane 70 a kauyen mais uma Zaongo, duk da yake sanarwar ta ce akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya zarta haka lura da cewa akwai wadanda suka samu munanan raunuka. 

Bayanai dai na nuni da cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu yara kanana ne da kuma tsofaffi, sannan kuma har yanzu ba a tantance wadanda suka aikata wannan mummunan kisa ba. 

A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar da sanarwa inda a ciki ta bukaci mahukuntan kasar ta Burkina Faso da su fito su yi wa duniya karin bayani a game da rahotannin da ke cewa an kashe mutane kusan 100 a kauyen na Zaongo, to sai dai mahukuntan ba su mayar da martani ba sai a yammacin wannan litinin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.