Isa ga babban shafi

Shugaban Ghana ya nemi hadin kan Duniya wajen tunkarar matsalar ta'addanci

Shugaba Nana Akufo-Addo ya bukaci hadin kan kasashen Duniya don tunkarar barazanar tsaro daga ayyukan kungiyoyi masu rike da makamai wadanda ke ikirarin jihadi a kasashen yammacin Afrika, matsalar da shugaban ke cewa ta na ci gaba da tunkaro Ghana da makwabtanta.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. AFP - JOHN ANGELILLO
Talla

A cewar shugaban yayin jawabinsa a birnin Washington DC na Amurka, ya ce sannu a hankali matsalolin ta’addanci daga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addini na ci gaba da gangarowa daga yankin Sahel zuwa sauran sassan nahiyar.

Shugaban na Ghana, cikin jawabin nasa ya kwatanta yadda taimakon da kasashen yammacin Afrika ke bukata wajen yaki da ta’addanci da irin taimakon da kasashen yammaci ke baiwa Ukraine a yakin da ta ke da Rasha.

Nana Akufo-Addo ya ce anzo gabar da dole sai an hannu don magance matsalolin tsaro da tarnaki da ke tunkaro mulkin demokradiyya baya ga yaki da tsattsauran ra’ayi a kasashen yammacin nahiyar ta Afrika.

Zuwa yanzu dai, tarin ‘yan ta’adda ke rike da yankuna da dama na kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, dai dai lokacin da Amurka da kawayenta ke kokarin taimakawa Ghana da makwabtanta wajen karfafa tsaron Sojin da nufin ganin bata ci karo da matsalolin hare-haren ta’addancin ba.

Matsalolin ta’addancin dai tuni suka fara fantsamuwa kasashen Togo da Benin da kuma Ivory Coast wadanda dukkaninsu suka ga hare-haren ta’addanci a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.