Isa ga babban shafi

Ta'addanci: Masallatai da Majami'un Uganda za su fara tantance sabbin fuskoki

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya roki al’ummar kasar da su kasance a ankare sakamakon rahotannin yiwuwar samun hare-haren ta’addanci a sassan kasar, ya na mai cewa dole wuraren bauta su sanya idanu kan sabbbin fuskokin da za su halarci wuraren tare da tantance su.

Wani Masallaci a birnin Kampala na Uganda.
Wani Masallaci a birnin Kampala na Uganda. © Wikimedia Commons CC-BY-SA 4.0 Alvinategyeka
Talla

A wani jawabin kai tsaye da ya gabatar ta gidan talabijin shugaba Museveni ya roki Masallatai da Majami’u su sanya ido kan sabbin fuska tare da dakile duk wani da basu yadda da shi ba, daga shiga wuraren bautar da kuma mika shi ga jami'an tsaro matukar suka ga alamun nuku-nuku a tare da shi.

Kalaman na shugaba Museveni na zuwa ne bayan rahotannin hukumomin tsaron kasar da ke nuna yiwuwar samun hare-haren ta’addanci a kasar da ke dunkule da mabiya addinai daban-daban.

A cewar Museveni nauyi ne akan al’ummar kasar su sanar da jami’an tsaro, matukar suka samun halartar sabbin fuskokin da ba su yarda da su ba a wuraren bautar na su.

Haka zalika, Museveni ya kuma bukaci otel-otel da sauran wuraren shakatawa ko na saukar baki da su dauki cikakkun bayanan duk wani bako da ya yada zango a wuraren tare da tabbatar da sun bayar da katunan shaida da ke dauke hotuna da bayanansu a jiki gabanin basu masauki

A cewar sa dole ne sai masallatai da majami’u sun kange bakin fuska tukuna za a iya nasarar dakile barazanar ta ‘yan ta’adda da galibi kan fake da addini wajen kai hare-hare.

Shugaba Yoweri Museveni na wannan batu ne bayan jami’an tsaron Uganda sun yi nasarar kwance wani bom da aka nufaci tayarwa a wata majami’a da ke birnin Kampala baya ga gano wasu bama-baman na daban kwana guda a tsakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.