Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane da dama a Burkina Faso cikin mako guda - Rahoto

Sojoji da fararen hula da dama ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hare-haren ‘yan bingida a Burkina Faso a cikin  mako guda, kamar yadda majiyoyin tsaro da na yankunan da abin ya faru suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore. © AFP
Talla

Majiyoyin sun ce daga ranar Lahadin makon daya gabata kawo yanzu, akalla hare-hare hudu ne aka kai kan dakarun sojin kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dama akasarinsu a arewacin kasar.

Wata majiya daga yankin ta ce wasu gungun 'yan ta'adda dauke da muggan makamai sun kai hari a sansanin soji da ke Nouna a shiyar arewa maso yammacin kasar a ranar Asabar, inda sojoji da fararen hula da dama suka rasansu a artabun da aka yi tsakanin bangarorin biyu.

Haka nan wata majiyar tsaro da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ta tuntuba ta tabbatar da labarin kai harin, sannan kuma ta ce akwai wani harin da aka kai wa sansanin sojoji da ke Arewacin kasar duk a lokaci guda, sai dai ta ce sojojin sun yi kokarin dakatar da maharani.

Kungiyar masu ikirarin jihadi ta GSIM wacce ke da alaka da Al-Qaeda ce ta dauki alhakin kai harin, inda  ta yi ikirarin kashe sojoji kusan 60.

Gwamnatin sojojin kasar dai bata bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, duk da cewar kafar Talabijin ta kasar ta ce an kashe ‘yan ta’adda kusan 30  tare da lalata sansanoninsu uku da sojoji suka gano a shiyar Arewa maso Yammacin kasar.

Tun a sheakarar 2015 ce dai Burkina Faso ta fara fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi, wadanda ke da alaka da kungiyoyin IS da Al-Qaeda kuma tuni suka bazu zuwa kasashen Mali da Nijar da ke makwabtaka ta ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.