Isa ga babban shafi

‘Yan ta’adda sun kashe jandarmomi 13 a Burkina Faso

‘Yan ta’adda sun kashe jandarmomi akalla 13 a wani harin kwanton bauna da suka kai ranar Lahadi a Taparko, wani gari mai filin hakar ma’adinai a arewacin  Burkina Faso.

Sojoji daga Burkina Faso yayin sintiri a kan hanyar Gorgadji a Burkina Faso, Maris 3, 2019.
Sojoji daga Burkina Faso yayin sintiri a kan hanyar Gorgadji a Burkina Faso, Maris 3, 2019. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, maharan sun yi wa wata tawagar jami'an Jandarma a yankin Dori kwanton bauna ne da yammacin ranar Lahadi a kusa da Taparko.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa, baya ga kashe Jami’an Jandarmomin 13, wasu kimanin takwas ko sama da haka sun bace a harin, yayin da wasu takwas din suka jikkata.

Taparko wani gari ne da ake hakar ma'adanai a kai a kai wanda mayakan jihadi suka sha kaiwa hare-hare.

Hare-haren ta'addanci na neman tsananta a Burkina

Harin da ya halaka Jandarmomin Burkina Fason ya zo ne, a daidai lokacin da wasu mutane biyu suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wata motar bas ta taka nakiya a ranar Lahadi, lamarin da shi ma ya auku. a kusa da garin na Taparko.

A ranar Asabar kuwa mutane 11 ‘yan ta’adda suka kashe a wani hari da suka kai kan wata mahakar zinari a Baliata, da ke arewacin kasar. Wani ganau ya shaida wa AFP cewa wasu mahara 30 ne kan Babura suka kai farmakin.

Burkina Faso dai na fama da hare-haren 'yan ta’adda masu ikirarin jihadi tun a shekara ta 2015, lokacin da mayakan da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS suka fara kai hare-hare kan iyakokin kasar daga Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.