Isa ga babban shafi
Burkina-Ta'addanci

'Yan ta'adda sun hallaka mayakan sa kai 13 a Burkina Faso

Rahotanni daga Burkina Faso sun ce 'yan ta’adda sun kashe wasu mayaka 'yan sakai 13 da ke taimakawa wajen samar da tsaro a yankin arewacin kasar.

Sojojin sa kai da ke tallafawa dakarun Burkina Faso yaki da ta'addanci.
Sojojin sa kai da ke tallafawa dakarun Burkina Faso yaki da ta'addanci. © Issoufou Sanogo
Talla

Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan sauke gwamnatin kasar da shugaba Roch Christian Marc Kabore ya yi, sakamakon matsin lamba daga jama’a kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Shugaba Kabore ya karbi takardar murabus daga Firaminista Christophe Joseph Marie Dabire a ranar laraba, domin kwantar da hankalin jama’a sakamakon tashe tashen hankulan da suka yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 2 da kuma raba kusan miliyan guda da rabi daga matsugunan su a cikin shekaru 6.

Ana saran shugaba Kabore ya zabo sabon Firaministan da zai kafa gwamnati nan bada dadewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.