Isa ga babban shafi
Burkina Faso

'Yan sandan Burkina Faso sun dakile zanga-zangar adawa da gwamnati

'Yan sandan Burkina Faso sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin kasar a ranar Asabar.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Burkina Faso a shekarar 2014, (An yi amfani da wannan hoto domin misali.
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Burkina Faso a shekarar 2014, (An yi amfani da wannan hoto domin misali. © Issouf Sanogo/AFP/Getty Images
Talla

Jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzomar sun harba barkonon tsohuwar ne domin hana masu zanga-zangar taruwa a dandalin da ke tsakiyar birnin Ouagadougou, inda aka jibge jami’an tsaro na musamman tare da rufe dukkanin shaguna.

Dandazon Jama'ar dai sun so su gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gazawar shugaba Roch Marc Christian Kabore kan dakile tashe-tashen hankulan da 'yan ta’adda masu ikirarin jihadi ke haddasawa da suka dabaibaye sassan kasar, amma kuma hukumomin tsaron suka dakile yunkurin.

Gamayyar kungiyoyin fararen hula uku ne suka shirya jagorantar zanga-zangar lumanar ta ranar Asabar din 27 ga watan Nuwamba, don yin tir da karuwar rashin tsaro tare da neman shugaba Kabore ya yi murabus.

Burkina Faso's President Roch Marc Christian Kabore won re-election by gaining enough votes on Sunday to avoid a run-off
Burkina Faso's President Roch Marc Christian Kabore won re-election by gaining enough votes on Sunday to avoid a run-off Issouf SANOGO AFP/File

Sai dai sauran kungiyoyin fararen hula sun nisanta kansu daga zanga-zangar, saboda a cewarsu, yin hakan zai iya jefa Burkina Faso cikin karin rudani.

Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama sun addabi al'ummar kasar ta Burkina Faso da ke yankin Sahel tun daga shekara ta 2015, inda suka kashe mutane kusan dubu 2 tare da raba wasu akalla miliyan 1 da dubu 400 da gidajensu.

A wani hari da mayaka masu yawa suka kai a ranar 14 ga watan Nuwamba, kan wani sansanin Jandarma dake Inata a arewacin kasar, inda suka kashe 'yan sanda 53 da wasu mutane hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.