Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Sojin Faransa sun kashe 'yan ta'adda 20 a iyakar Nijar da Mali

Ma’aikatar tsaron Faransa, ta ce jiragen yakinta sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 20 a wani yanki da ke jamhuriyar Nijar kusa da iyakokin kasar da Mali da Burkina Faso.

Wasu dakarun Sojin Faransa da ke yaki da ta'addanci a Sahel.
Wasu dakarun Sojin Faransa da ke yaki da ta'addanci a Sahel. AP - Jerome Delay
Talla

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Faransa kanar Pascal Ianni ya fitar a yau alhamis, ta ce an yi amfani da jiragen yaki da kuma marasa matuka samfurin Reaper don kai farmaki kan maboyar mayakan EIGS da ke matsayin reshen IS a yankin Sahara, inda aka kashe baraden kungiyar fiye da 20.

Wannan dai yanki ne da ya yi kaurin suna sakamakon yawaitar samun hare-hare daga kungiyoyin da ke da’awar jihadi tsakanin Burkina Faso, Mali, da kuma Jamhuriyar Nijar.

Tun cikin watan yunin da ya gabata ne Faransa ta fara sauya salon yadda dakarunta na Barkhane ke gudanar da ayyukansu a yankin Sahel, tare da janye wani adadi na sojojin daga Kidal, Tumbuktu da kuma Tessalit, bisa hasashen cewa za ta rage dakarun daga dubu 5 zuwa dubu 300 nan zuwa shekara ta 2023.

Tun shekara ta 2013 ne dai Faransa ta tura dubban sojojinta zuwa Mali don yaki da ayyukan ta’addanci, kafin daga bisani a fadada ayyukan sojin zuwa kasashe makota da suka hada da Nijar da kuma Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.