Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Burkina Faso ta yi jana'izar jami'an tsaronta da aka kashe

Burkina Faso ta binne wasu daga cikin Jandarmominta 49 da aka kashe a wani harin baya-bayan nan da aka kai kan wata cibiyar tsaro, adaidai lokacin da gwamnati ta sanar da kashe wasu karin jami’an tsaro da fararen hula kusan 20 a wani harin na daban.

Sojojin Burkina Faso dake sintiri kusa da sansanin da dakarun Faransa suka janye 20/11/21.
Sojojin Burkina Faso dake sintiri kusa da sansanin da dakarun Faransa suka janye 20/11/21. © OLYMPIA DE MAISMONT / AFP
Talla

Harin na ranar 14 ga watan Nuwamba a kusa da garin Inata dake arewacin Burkina Faso, wanda yayi sanadiyar mutuwar fararen hula hudu baya ga jandarmomi 49, shi ne mafi muni da jami'an tsaron kasar suka gani a 'yan shekarun baya-bayan nan.

Dubban ‘yan uwa da dangi dake cikin yanayin jimami ne dai suka ga yadda makarar gawakin ‘yan uwansu akalla 30 cikin manyan motoci dauke da tutar Burkina Faso a kan hanyarsu ta zuwa makabarta da ke Ouagadougou babban birnin kasar domin jana’izar bai daya.

Gazawar shugaba Kabore

Yawaitan hare-haren na zubar da jini da ke kara ta'azzara ya haifar da zanga-zanga da kuma kira ga shugaba Roch Mach Kabore da ya yi murabus saboda gazawar mahukuntan kasar wajen shawo kan rikicin da mayaka masu ikirarin jihadi ke kaiwa tsawon shekaru hudu da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilastawa sama da miliyan guda barin gidajensu.

Al’ummar kasar sun kara fusata sakamakon rahotannin da ke cewa yunwa ya tilastawa da jami’an Jandarmomi neman abinci kusa da sansanin kafin kaimu harin.

Zanga-zangar adawa da sojojin Faransa

Sakamakon zanga-zangar adawa da gwamnatin Burkina Faso da sojojin Faransa na baya-bayan nan, hukumomin kasar sun katse kafar intanet ta wayoyin salula a fadin kasar da ke yammacin Afirka, bayan da sukayi amfani da wani tanadin doka da ya shafi tsaron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.