An harbe mutane 4 yayin zanga-zangar kin jinin sojojin Faransa a Burkina Faso
Wasu majiyoyi daga kasar Burkina Faso suka ce akalla mutane hudu suka samu rauni, bayan da dakarun kasar da na Faransa suka bude wuta a kokarin dakile masu zanga-zangar da ke kokarin toshe ayarin motocin sojojin Faransa.
Wallafawa ranar:
Wata majiya a garin Kaya da ke arewacin babban birnin kasar ta ce masu zanga-zangar sun yi kokarin tunkarar jami'an sojojin Faransa a wani yanki da suka shafe dare.
Majiyar lafiya ta ce "ma'aikatar gaggawa ta asibitin Kaya ta karbi mutane hudu da suka samu raunukan harbin bindiga".
Sai dai wata majiyar sojan Faransa ta musanta cewa an jikkata mutane, inda ta yi watsi da alhakin abin da ya wakana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu