Isa ga babban shafi
Faransa-G5

Faransa za ta jagoranci taron kasashen G5 Sahel a Chadi

Faransa da kawayenta 5 na yankin Sahel za su gudanar da taron kwanaki biyu a Ndjammena babban birnin kasar Chadi, a wata mai kamawa don tattauna batutuwa da suka shafi rikicin yankin.

Taron kasashen G5 Sahel a Mauritania.
Taron kasashen G5 Sahel a Mauritania. Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Sanarwar fadar gwamnatin Faransa da ke tabbatar da batun taron ta ce Shugabancin kasar zai yi amfani da damar wajen ganawa da shugabannin kasashen 5 a ranakun 15 da 16 ga watan Fabairu mai kamawa, ko da yake sanarwar bata bayyana ko shugaban kasar Emmanuel Macron zai halarci taron na Njammena ba.

A Shekara da ta gabata shugaban Macron ya karbi bakwancin taron shugabannin kasashen na G5 Sahel da suka hada da Mauritania da Burkina Faso da Mali da Niger da kuma Chadi a birnin Pau da ke kudancin Faransa.

Taron wanda ke zuwa a dai dai lokacin da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi a yankin ke zama tamkar ruwar dare, zai tattauna batutuwa da suka shafi lamarin da rikicin siyasar yankin, sai kuma batun rage adadin dakarun Faransa da ke cikin rundunar Barkhane mai yaki da ta’addanci.

Yanzu haka dakarun Faransa kimanin dubu 5 ke cikin rundunar ta Barkhane don taimakawa takarorinsu na kasashen yankin wajen fafatawa da mahara masu ikirarin jihadi, to sai dai kasar na neman rage adadin don karasu ga kawancen Turai na kasa-da-kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.