Isa ga babban shafi

An bude taron G5 Sahel a Nouakchott

Shugabannin kasashe biyar na kungiyar G5-Sahel, na gudanar da taron yau Talata a birnin Nouakchott fadar gwamnatin kasar Mauritaniya don tattauna batutuwan da suka shafi fada da ayyukan ta’addanci a yankin, taron da ke samun halartar shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda a karon farko ke ziyarar wata kasa da ke wajen yakin Turai.

Wani sojan Faransa na Barkhane a yankin Sahel
Wani sojan Faransa na Barkhane a yankin Sahel AFP Photo/MICHELE CATTANI
Talla

Wasu daga cikin mahalarta taron sun hada da Moussa Faki Mahamat shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, da Louise Mushikiwabo ta kungiyar kasashe renon Faransa OIF, sai kuma Firaministan Spain Pedro Sanchez.

Hakazalika an fadada wannan taro ta hoton bidiyo domin bai wa shugabannin Jamus da Italiya damar bayyana mahangarsu kan abubuwan da ke faruwa a yankin na Sahel.

Watanni 6 da suka gabata ne shugabannin kasashen Sahel 5, Burkina Faso, Chad, Mali, Nijar da Mauritania suka gana da shugaba Macron a garin Pau da ke Faransa, tare da shata wasu manufofi kan yadda za a yaki ayyukan ta’addanci a Sahel.

A lokacin wannan taro ne dai shugabannin suka sanar da sabbin matakai na yaki da ayyukan ta’addanci musamman a kusurwar kasashe 3 da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso, yayin da Faransa ta sanar da kara sojoji 500 zuwa yankin baya ga wasu dubu 4 da 500 da ke aiki karkashin rundunar Barkhane.

A cikin ‘yan watanni da suka gabata, rundunar ta Barkhane sojojin kasashen yankin sun yi ikirarin kashe daruruwan ‘yan ta’adda ciki har da jagoran kungoyar Aqmi wato Abdelmalek Droukdel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.