Isa ga babban shafi
Sahel

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin fasakwauri a Sahel

Rahotanni daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar sun ce wani fada da ya barke tsakanin kungiyoyin da ke safarar makamai da kwayoyi a kusa da iyakar Libya da Algeriya ya yi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

Taswirar yankin Sahel mai fama da rikicin ta'addanci.
Taswirar yankin Sahel mai fama da rikicin ta'addanci. RFI
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar tsakanin Alhamis da juma’ar da suka gabata, an samu fafatawa tsakanin kungiyoyin da ke safara a yankin inda aka kashe mutane sama da dozin guda.

Wani jami’in yankin Agadez ya ce daya daga cikin bangaren kungiyoyin ne ya yi kwantan bauna inda ya kai hari ga dayan a kokarin mamaye safarar makamai da kwayar da ake yi a yankin.

Wata majiya ta ce mutanen da aka kashe sun kai 17 daga bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.