Mai yiwuwa kasashen Turai su yafe bashin da suke bin yankin Sahel
Kasashen dake kungiyar tarayyar Turai EU, sun ce zasu tattauna bukatar yafewa kasashen Sahel bashin da suka gabatar, bayan tattaunawar da aka yi ta bidiyo tsakanin shugabannin kasashen yankin da kuma shugaban majalisar Turai Charles Michel.
Wallafawa ranar:
Michel yace kasashen Sahel da suka hada da Mauritania, Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Chadi na fuskantar yaki da yan ta’adda a kusan shekaru 8 da suka gabata.
Jami’in yace bayan tattaunawar da suka yi a tsakanin su, yanzu sun amince su gudanar da taro akai tare da abokan huldar su irin su hukumar IMF domin daukar matsayi akai.
Kasashen duniya na kallon nahiyar Afirka a matsayin yankin da annobar coronavirus za tayi matukar illa saboda rashin harkokin kula da lafiya masu inganci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu