Isa ga babban shafi
Duniya

Kasashen Duniya za su tallafawa G5 Sahel da dala miliyan 500

Masu bayar da agaji na kasashen duniya sun yi alkawarin taimakawa rundunar yaki da yan ta’addar da wasu kasashe 5 na Afirka suka kafa da ake kira G5 Sahel da kudin da ya zarce Dala miliyan 500. Jami’an kungiyar kasashen Turai sun ce rundunar za ta taimaka sosai wajen dakile baki da kuma masu aikata laifufuka zuwa kasashen su.

Le président du G5 Sahel et chef d'Etat nigérien Mahamadou Issoufou (2e à gauche), le président de la Commission européenne Jean-Claude Juncker (centre) et la cheffe de la diplomatie européenne Federica Mogherini (droite), à Bruxelles le 23 février 2018.
Le président du G5 Sahel et chef d'Etat nigérien Mahamadou Issoufou (2e à gauche), le président de la Commission européenne Jean-Claude Juncker (centre) et la cheffe de la diplomatie européenne Federica Mogherini (droite), à Bruxelles le 23 février 2018. REUTERS/ John Thys/Pool
Talla

Akalla kasashe 50 ne suka yi alkawarin ba da kudin da ya kai Dala miliyan 509 don gudanar da ayyukan rundunar, kuma kasashen sun hada da Amurka da Japan da Norway.

Kungiyar kasashen Turai ta bayar da euro miliyan 116 domin ganin sojojin Turai sun janye nan da karshen wannan shekara.

Shugabar kungiyar diflomasiyar kasashen Turai, Federico Mogherini ta bukaci ganin kasashen da suka yi alkawarin sun gaggauta bada kudaden domin kai wa ga sojojin da za su yi aikin.

Kasar Faransa ta bayyana farin cikin ta da kudaden da aka tara, bayan an kwashe shekaru ana ta kokarin kafa rundunar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyaan cewar, sojojin kasar sa za su ci gaba da aiki tare da na kungiyar G5 Sahel domin murkushe Yan ta’addan da ke Yankin.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da Firaministan Italia, Paolo Gentilino da na Spain Mariano Rajoy da kuma shugabannin kasashen Mali da Nijar da Chadi da Burkina Faso da kuma Mauritania sun halarci taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.