Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Burkina Faso ta kashe tarin 'yan ta'adda a wani sumamen hadin gwiwa

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da kashe tarin 'yan ta’adda da kuma kame wasu daruruwa sakamakon atisayen hadin gwuiwa da dakarun kasar suka kaddara tare da takwarorin su na kasashen Cote d’Ivoire da Ghana da kuma Togo a makon jiya.

Dakarun Sojin Burkina Faso.
Dakarun Sojin Burkina Faso. © MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Ministan tsaron Burkina Faso Maxime Kone ya ce daga ranar 21 ga watan Nuwamba zuwa 27 sojoji kusan dubu 6 daga kasashen 4 suka kaddamar da sintirin hadin gwuiwa, abinda ya basu damar kama mutane akalla 300 da ake zargin 'yan ta’adda ne.

Ma'aikatar tsaron Burkina ta ce yayin sintirin hadin gwiwar kasashen 4 sun kuma yi nasarar kwace makamai 53 da motoci da Babura 150 wadanda 'yan ta'addan kan yi amfani da su wajen kai farmaki.

Minista Maxime ya ce sun yi nasarar lalata sansanin 'yan ta’adda guda 5 a cikin kasar.

Burkina Faso na jerin kasashen yankin Sahel da ke fama da matsalar ayyukan ta'addanci duk da taimakon Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.