Isa ga babban shafi

Fashewar nakiya ya kashe fasinjoji 10 a Burkina Faso

Fasinjoji 10 da ke kan wata bas sun mutu a lokacin da motarsu ta taka wata nakiya a gabashin Burkina Faso.

Wasu jandarmomi a birnin Ouhigouya da ke Burkina Faso ranar 30 ga watan Oktoban 2018.
Wasu jandarmomi a birnin Ouhigouya da ke Burkina Faso ranar 30 ga watan Oktoban 2018. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Wata karamar motar bas hukumomi suka ce ta taka nakiya a kan wata hanya kusa da kauyen Bougui da yammacin ranar Lahadi, abin da  ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji 10, in ji gwamnan yankin Kanar Hubert Yameogo a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya kara da cewa, mutane 5 sun jikkata kuma tuni aka kai su asibiti da ke babban birnin yankin Fada N'Gourma, yayin da adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa yayin da ake kyautata zaton wasu fasinjojin sun bata.

Lamarin dai na zuwa ne bayan wani bam ya kashe sojoji biyu a kan hanyar arewacin Burkina Faso a ranar Asabar, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana wa AFP.

Tun a shekara ta 2015 ne dai kasar da ke yammacin Afirka ke fama da tashe tashen hankula a karkashin jagorancin masu tayar da kayar baya da ke alaka da Al-Qaeda da kuma kungiyar IS wanda ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane tare da raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu.

Hare-haren da ake kaiwa jami'an tsaro da fararen hula na karuwa a 'yan watannin nan, musamman a yankunan arewaci da gabashin kasar da ke kan iyaka da Mali da Nijar, wadanda suma ke fafatawa da masu dauke da makamai.

Shugaban mulkin sojan Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya mayar da hankali sosai wajen kwato yankunan da ke karkashin ikon masu dauke da makamai.

Gazawar gwamnati wajen dakile hare-haren masu jihadi ya taka muhimmiyar rawa a juyin mulkin da sojoji suka yi har sau biyu a Burkina Faso a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.