Isa ga babban shafi
Mali

Kofar ragon da mayaka ke yi wa Menaka ya jefa al'ummar garin cikin kunci

Rahotanni daga gabashin Mali na nuni da cewa mazauna birnin Menaka da kewayensa na rayuwa cikin kunci na  karanci da kuma tsadar abinci, magunguna, da man fetur, sakamaka kawanyar da kungiyoyin mayaka masu ikirarin Jihadi da kuma na ‘yan tawaye suka yi wa yankin nasu.

Wani kauye da ke kusa da garin Menaka a kasar Mali. 28 ga Oktoba, 2021.
Wani kauye da ke kusa da garin Menaka a kasar Mali. 28 ga Oktoba, 2021. © FLORENT VERGNES / AFP
Talla

Tun cikin watan Afrilun shekarar bara ne dai mayakan IS suka kawce iko da baki dayan yankunan da ke kewaye da birnin na Menaka, ciki har da baki dayan hanyoyin da ke sada garin da jamhuriyar Nijar.

Bayan tashin hankalin da aka gani ne kuma, a karshen watan Satumba, mayakan kungiyar Jnim mai alaka da Al Qa’eda suka sanar da nasu matakin na datse hanyoyin shiga birnin Menakan, yayin kuma a watan Disamba ‘yan tawayen CSP da suka fice daga yarjejeniyar sulhun shekarar 2015 da gwamnatin Mali, su ma suka sanar da nasu takunkuman da suka kakaba kan garin.

Wasu mazauna yankin da gidan rediyon RFI ya tuntuba sun ce tuni man fetur ya zama tamkar Zinare, bayan da farashinsa ya tashi daga kasa da kudin Franks dubu 1 zuwa sama da dubu 4000 kan kowace lita guda, yayin da farashin shinkafa ya ninka fiye da su biyu.

Kuncin tsadar rayuwar na kara yin muni ne kuma la’akari da cewar, yanzu haka mazauna garin na Menaka na karbar bakuncin ‘yan gudun hijira fiye dubu 45 da matsalolin tsaro suka tilasta wa gujewa muhallansu daga sassan Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.