Isa ga babban shafi

Sama da mutum miliyan 8 ne ke bukatar agajin gaggawa a Mali - WFP

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, tace sama da mutum miliyan takwas da dubu dari takwas ne ke bukatar agajin jin kai a kasar Mali a shekarar 2023, adadin da tace yah aura sama da wanda aka samu a shekarar 2022.

Wani sashe na sansanin yan gudun hijirar Mali da ke Sevare, mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso gabashin birnin Bamako.
Wani sashe na sansanin yan gudun hijirar Mali da ke Sevare, mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso gabashin birnin Bamako. Reuters/Emmanuel Braun
Talla

 

Daga cikin mutum miliyan daya da dubu 26 da WFP ta shirya tallafawa a barra, mutum dubu 464 aka tabbatar sun ci gajiyar shirin, wanda hakan ke nufin kaso 37 ne kacal suka samu wannan tallafin na jin kai.

Hukumar ta ce ta fi mayar da hankali ga al’ummar yankin Menaka wajen bayar da agajin gaggawa na abinci da kuma sauran abinci mai gina jiki, inda a watan Satumba kadai aka taimakawa sama da mutum dubu 640 na abinci.

Rahoton hukumar ya ci gaba da cewa, sama da yara dubu 90 ne ‘yan tsakanin watanni shida zuwa 23 aka rabawa magungunan gina jiki, inda mata masu juna biyu da kuma wadanda ke shayarwa aka tallafa musu da kudade domin kula da lafiyarsu.

Daga farkon shekarar 2023 zuwa yanzu, sama da mutum miliyan biyu da dubu 200 ne WFP ta tallafawa a kasar Mali, inda aka ware sama da dala miliyan 61 domin tallafawa mutanen da ke cikin tsananin bukata daga nan zuwa watanni shida masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.