Majalisar Sojin Mali ta kawo karshen yarjejeniyar Algiers da aka rattabawa hannu a 2015 da Abzinawa
A kasar Mali,majalisar soji ta sanar da kawo karshen tare da aiwatar da matakin nan take na yarjejeniyar Algiers da aka rattabawa hannu a shekarar 2015 da kungiyoyin Abzinawa masu neman 'yancin kai a arewacin kasar.
Wallafawa ranar:
A cikin sanarwa da suka fitar zuwa manema labarai , Mali ta bayyana abin rashin jin daɗi,ganin rawar da makwabciyarta Aljeriya ke takawa a bangaren da ya shafi Hulda da sanin abinda ya dace tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya hannu a shekarar 2015 tsakanin kasar Mali da kungiyoyin 'yan tawaye, ta kasance marar tushe, in ji sanarwar da aka fitar wacce ke nuna karshenta a hukumance.
Don tabbatar da wannan matsayi, gwamnatin soji ta nuna damuwa ganin rawar da wasu kungiyoyin Abzinawa ke takawa tare da canza salo a fuskoki da dama.
Majalisar Soji ta yi tir da wasu daga cikin manufofi na nuna kyama da cin zarafi daga hukumomin na Algeria.
Hukumomin Mali na danganta kungiyoyin Abzinawa da suka bijerewa dokokin kasar ta Mali a matsayin yan ta'adda".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu