Isa ga babban shafi

MDD ta mika ikon sansanin Timbuktu ga hukumomin Mali bayan ficewar sojojinta daga kasar

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali (MINUSMA) ta mika iko da daya daga cikin manyan sansanonin ta na karshe a yankin Timbuktu da ke arewacin kasar.

Sojojin kasar Chadi kenan yayin wani aikin sintiri da dakarun MINUSMA na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 25 ga Oktoba, 2023.
Sojojin kasar Chadi kenan yayin wani aikin sintiri da dakarun MINUSMA na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 25 ga Oktoba, 2023. AFP - -
Talla

Tawagar ta MINUSMA da ta dauki tsawon shekaru goma ana sa ran z ata mika sansanin na Gao da Timbuktu ga hukumomin Mali a watan Janairu.

Sai dai yanayin rashin tsaro da ake fama da shi a yankin da ake fama da hare-haren masu tayar da kayar baya, ya sanya dakarunta kara ja da baya daga Timbuktu.

Wata majiyar Majalisar Dinkin Duniya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, t ace saboda rashin samun mafita ga sha’anin tsaro a sansanin MINUSMA da ke Timbuktu, ya zama dole a rufe wannan sansanin cikin gaggawa.

Faifan bidiyo ya nuna yadda gwamnan yankin, Bakoun Kante, ke mika godiya ga Majalisar Dinkin Duniya a yayin wani bikin karbar ikon yankin a hukumance.

Rundunar sojan Mali ta bukaci MINUSMA da ta janye cikin gaggawa a watan Yunin da ya gabata sakamakon tabarbarewar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu da aka samu.

MINUSMA ta yi asarar rayuka kusan 180 a cikin shekaru 10 da ta yi kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel mai fama da tashin hankali daga kungiyoyin masu dauke da makamai.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen wa'adin da aka jibge kusan dakaru 15,000 a ranar 30 ga watan Yuni, ya kuma ayyana wa'adin ranar 31 ga watan Disamba a matsayin lokacin da tawagar ta MINUSMA z ata fice daga kasar.

A makon da ya gabata ne dakarun Abzinawa 'yan aware suka ce suna tare hanyoyi a yankin.

An sake gwabza fada tsakanin 'yan awaren da sojojin gwamnati a cikin watan Agusta bayan shafe shekaru takwas ana kokarin kwantar da hankula, a daidai lokacin da bangarorin biyu suka yunkuro domin cike gibin da janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ya bari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.