Isa ga babban shafi

MINUSMA ta sauke tutarta a Mali bayan kawo karshen aikinta

Dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Mali MINUSMA sun sassauta tutar majalisar dinkin duniya a shalkwatar ta da ke birnin Bamako, abinda ke nufin ana gab da kawo karshen shekara 10 da tawagar ta dade tana aiki a kasar.

Dakarun na ci gaba da fice sannu a hankali daga Mali
Dakarun na ci gaba da fice sannu a hankali daga Mali © RFI
Talla

Yayin bikin sassauta tutar a kasar da ke fama da ayyukan ta’addanci, kakakin dakarun wanzar da zaman lafiyar Fatoumata Kaba ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa har yanzu akwai wasu kananan sansanonin sojojin da ba’a kai ga kammala rufewa ba.

Tun shekarar 2013 ne tawagar da dirá a Mali da sunan yaki da ta’addanci, sai dai kuma babu wani sauki da aka samu, la’akari da yadda ‘yan ta’adda ke kai hare-hare a sassan kasar dake zaman guda cikin masu fama da talauci a yankin Sahel.

 

Taswirar kasar Mali
Taswirar kasar Mali © Studio graphique FMM

Kidddiga ta nuna cewa hare-haren ta’addancin ya raba miliyoyin mutane da muhallan su yayin da wasu dubbai suka rasa rayukan su dungurungum, duk kuwa da kasancewar sojojin Minusma fiye da dubu 15 a kasar.

 

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, sun bukaci dukannin dakarun majalisar dinkin duniya da su fice, saboda zargin basa aikata komai sai ma ta’azzara matsalolin tsaron a wasu lokutan.

Sojojin na zargin dakarun na Minusma da ta'azzara matsalar tsaro
Sojojin na zargin dakarun na Minusma da ta'azzara matsalar tsaro RFI/David Baché

Sai dai kuma masana harkokin tsaro sun dade suna shaida cewa aikin MINUSMA ba shi ne yaki da ta’addanci ba, sai dai tabbatar da tsaro don haka bai kamata a zarge su dan basu dauki bindgiga sun yaki ‘yan ta’adda ba.

Ko da yake nasa jawabi shugaban dakarun na MINUSMA a Mali El Ghassim Wane ya ce tawagar ta samu nasara matuka a Mali, don haka akwai takaici yadda zasu fice kan dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.