Isa ga babban shafi

Ficewar rundunar MINUSMA daga Mali ya haifar da rudani

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kafin dakarun ta na wanzar da zaman lafiyar su gaggauta ficewa daga sansaninsu da ke Kidal na Arewacin Mali a ranar Talatar data gabata, sai da su ka lalata wasu muhimman na’urorinsu don gudun fadawa hannun bata gari, lamarin da ya haifar mata da asara.

Wata daga cikin motocin sojojin MINUSMA a Mali.
Wata daga cikin motocin sojojin MINUSMA a Mali. AFP/Archivos
Talla

Jim kadan bayan ficewar ayarin karshe na motocin Majalisar Dinkin Duniya daga sansanoninsu, 'yan tawayen Abzinawa sun sanar da karbe iko dasu, kamar yadda hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Laraba sun nuna yadda mutanen yankin ke dorawa manyan motoci kayayyakin da suka kwashe daga ciki.

A watan Yuni ne gwamnatin mulkin sojan Mali, ta umurci sojojin Majalisar Dinkin Duniya da suka kwashe shekaru 10 suna aikin wanzar da zaman lafiya a kasar su fice daga cikinta, sakamakon tsamin da dangantakartar da ke tsakaninsu ta yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta gaggauta jaye dakarunta da ke aiki a karkashin MINUSMA a 'yan makonnin da suka gabata, bayan da rikici ya kaure a arewacin Mali tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar, da ke fafutukar neman rike ikon yankunan da Majalisar Dinki Duniya ta fice daga cikinsu.

Wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya ta kai tsaye kan janyewar sojojin Majalisar Dinkin Duniya, sun ce ana tafaka rikici a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya biyu, sannan kuma an yi awon gaba da kayayyakin da ke cikin wasu biyu.

Rundunar MINUSMA da ke aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta fuskanci kalubale a yayin ficewar ta daga kasar, inda aka tilasta mata lalata kayan aiki da suka hada da motoci da janareta, sakamakon yadda gwamnatin sojin kasar ta sanya dokar hanasu fitar da kayan.

Mai magana da yawun rundunar Fatoumata Sinkoun Kaba, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa sun yi asarar kayayyakin aiki na miliyoyin daloli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.