Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Mali sun mamaye sansanin dakarun MDD

‘Yan tawayen Mali da ke fafutukar ballewa daga kasar sun yi ikirarin mamaye wani sansani a birnin Kidal jim kadan da ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu daga cikin 'yan tawayen Abzinawa a Mali
Wasu daga cikin 'yan tawayen Abzinawa a Mali © Soumeylane Ag Anara / AFP
Talla

Wannan wata gagarumar alama ce da ke nuna yadda ‘yan tawayen suka zafafa fafutukarsu ta kafa yankinsu don cin gashin kansu.

‘Yan tawayen dai sun mamaye sansanin ne wanda dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka zauna a cikinsa, kafin ficewarsu a jiya Talata.

Gamayyar kungiyoyin ‘yan tawayen da akasarin mambobinta Abzinawa ne da suka kaddamar da wani shiri na saka kafar-wando daya da gwamnatin Mali ta ce, tuni ta karbe iko da wuraren da rundunar MINUSMA ta fice daga cikinsu a birnin Kidal.

Ayarin rundunar ta MINUSMA da ta kunshi sama da motoci 100 ta fice daga wannan sansanin ne cikin tsari, inda ta doshi birnin Gao mai tazarar kilomita 330 daga Kidal.

Sansanin dai shi ne na uku kuma na karshe da ya rage a hannun dakarun na Majalisar Dinkin Duniya a Kidal da ke yankin arewacin Mali mai fama da rikicin mayakan jihadi.

Da ma jim kadan da juyin mulkin da aka yi a shekarar 2020, sabuwar gwamnatin sojin Mali ta umarci dakarun na Majalisar Dinkin Duniya da su fice daga kasar, tana mai cewa, sun gaza a aikinsu na wanzar da zaman lafiya.

Rundunar ta MINUSMA mai kunshe da dakaru dubu 15 da suka hada da sojoji da ‘yan sanda, ta yi asarar mambobinta har guda 180 da aka kashe su a yayin gudanar da ayyukansu a Mali.

Tun da farko dai, an tsara cewa, wannan runduna za ta janye ne daga Mali nan da karshen shekarar nan, amma sannu a hankali dakarun suka fara ficewa daya bayan daya tun daga farkon watan Yulin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.